Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Hana Sana’ar Cajin Waya A Katsina


Gwamna Aminu Bello Masari (Facebook/Bello Masari)
Gwamna Aminu Bello Masari (Facebook/Bello Masari)

“Mun yi amannar cewa, sana’ar cajin waya, wani fanni ne da yake taimakawa ‘yan fashin daji wajen samun hanyoyin sadarwa.”

Gwamnatin jihar Katsina ta haramta sana’ar cajin waya a sassan jihar, a wani mataki na shawo kan matsalar tsaro da take addabar yankin.

Gwamna Aminu Bello Masari ne ya sanar da wannan sabon mataki yayin kaddamar da wani kwamitin da zai rika sa ido kan sabbin dokokin da aka kafa a jihar kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

“Umarni na baya-bayan nan da muka bayar ya hada da rufe duk wuraren da ake sana’ar cajin waya a yankunan da matsalar tsaro ta fi shafa.

“Mun yi amannar cewa, sana’ar cajin waya, wani fanni ne da yake taimakawa ‘yan fashin daji wajen samun hanyoyin sadarwa.”

Jaridar Daily Post wacce ita ma ta ruwaito labarin ta ce, kananan hukumomi 19 matakin zai shafa, wadanda ake sa ran kwamitin zai mayar da hankali akansu.

Gwamnan ya lissafo yankunan da dokar ta shafa, wadanda suka hada da Jibia, Batsari, Safana, Danmusa, Paskari, Sabuwa, Kurfi, Danja, Kaita, Bakori, Funtua, Kankara, Musawa, Matazu, Dutsima, Mai’adua, Malumfashi da Funtua.

Hukumomin jihar sun ce wannan mataki da wanda ma’aikatar sadarwa ta kasa ta dauka, zai taimaka mataka wajen rage ta’asar ‘yan bindiga a arewa maso yammacin jihar.

Masari ya kara da cewa, gwamnatin jiha za ta ci gaba da sa ido kan al’amuran da ke faruwa tare da kawo wasu sabbin tsare-tsare da za su taimaka wajen magance matsalar tsaro da jihar ke fuskanta.

Jihar Katsina ta kasance daya daga cikin jihohi a arewa maso yammacin Najeriya da ke fama da matsalar ‘yan fashin daji, inda a kwanakin baya gwamnan ya ce akwai yankunan da a kulliyaumin sai ‘yan bindiga sun kai masu hari.

XS
SM
MD
LG