Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rikicin Goma: Malawi Na Shirin Janye Dakarunta Daga Dimokiradiyyar Congo


Kasar Malawi ta umarci rundunar sojinta ta fara shirin janyewa daga gabashin Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo, yankin da kungiyar ‘yan tawayen M23 mai samun goyon bayan Rwanda ta kaddamar da sabbin hare-hare, a cewar fadar shugaban kasar.

Dakarun wani bangare ne na tawagar kungiyar raya kasashen kudancin Afrika (SADC) da aka tura su taimakawa gwamnatin Kinshasa kwantar da tarzoma a yankin gabashin kasar mai arzikin ma’adinai a 2023.

“Shugaba Lazarus Chakwera ya umarci kwamandan dakarun tsaron Malawi ya fara tsare-tsaren janyewa-domin mutunta ayyanawar tsagaita wuta,” kamar yadda fadar Chekwera ta bayyana da yammacin jiya Laraba.

Matakin zai kuma ba da damar “tsara tattaunawar samun zaman lafiya na dindindin”, kamar yadda fadar shugaba Chekwera ta kara bayyanawa.

Ba’a bayyana lokacin da dakarun zasu fara janyewa ba.

Kasar Afirka ta Kudu ce keda rinjayen dakaru a tawagar ta SADC, wacce aka kiyasta yawan dakarunta zasu kai 1, 300, inda Tanzaniya ma taba da gudunmowar sojoji.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG