Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Harin ‘Yan Fashi Da Makami A Kasuwar Yobe Ya Hallaka Mutane 7


Yan bindiga
Yan bindiga

Wasu da ake zargin ‘yan fashi da makami ne sun kai hari kan shahararriyar kasuwar nan ta Ngalda dake karamar hukumar Fika ta jihar Yobe, inda suka hallaka mazauna yankin 7.

An ce ‘yan fashin sun arce da Naira milyan 16.5 yayin harin daya faru a jiya Litinin sa’ilin da mazauna yankin ke tashi daga shahararriyar kasuwar ta ngalda, wani kauye dake kan iyaka da jihar Gombe.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Yobe, Dungus Abdulkarim, ya tabbatar da afkuwar lamarin a sanarwar daya rabawa manema labarai a yau Talata.

Ya kara da cewar an kama jagoran ‘yan fashin, Datti Alhaji Dadji, wanda mazaunin garin Ngaldan ne.

Yayin da yake janjatawa iyalan mutanen da harin ya rutsa dasu, kwamishinan ‘yan sandan jihar, Ahmad Garba, ya ba da umarnin gaggawa na gudanar da bincike kan lamarin tare da yin kira da kwantar da hankula.

Ya umarci jami’ansa su kama sauran mambobin gungun ‘yan fashin tare da yin kira ga jama’a da su taimakawa rundunar da sahihan bayanai.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG