A jiya Talata Namibia jam’iyyar SWAPO mai mulki a kasar Namibia ta lashe zaben shugaban kasa, inda 'yar takararta Netumbo Nandi-Ndaitwah, mai shekaru 72, za ta kasance shugabar kasar mace ta farko a kasar, kamar yadda sakamako da hukumar zabe ta fitar ya nuna.
Nandi-Ndaitwah mai shekaru 72 da haihuwa, ita ce mataimakiyar shugaban kasa ta yanzu.
Nasarar da ta samu za ta kara tsawon shekaru 34 da jam’iyyar SWAPO ta shafe tana mulki, tun bayan da ta jagoranci Namibia wajen samun ‘yancin kai daga mulkin wariyar launin fata a Afirka ta Kudu a shekarar 1990.
Ta samu kusan kashi 57% na kuri’un da aka kada a zaben shugaban kasar, kamar yadda hukumar zabe ta Namibia ta bayyana.
Nandi-Ndaitwah tana bukatar ta samu sama da kashin 50% na kuri’un da aka kada don ta yi nasara.
Babban abokin hamayyarta a wannan zabe shi ne Panduleni Itula daga jam’iyyar Patriots for Change (IPC), ya zo na biyu da kusan kashi 26% na kuri’un da aka kada.
Dandalin Mu Tattauna