Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zaben Ghana: Yadda Aka Rattaba Hannu Kan Yarjejeniyar Zaman Lafiya


Mataimakin Shugaban kasa, Bawamia, (Hagu) Tsohon Shugaban kasa Mahama, (Dama) (Hoto: Facebook/Dr. Mahamudu Bawamia)
Mataimakin Shugaban kasa, Bawamia, (Hagu) Tsohon Shugaban kasa Mahama, (Dama) (Hoto: Facebook/Dr. Mahamudu Bawamia)

A ranar 7 ga watan Disamba za a guduanar da zaben na shugaban kasa a kasar ta Ghana.

Mataimakin Shugaban Kasa, Dr. Mahamudu Bawumia, wanda shi ne dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar New Patriotic Party (NPP), da John Mahama, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar National Democratic Congress (NDC), sun jagoranci sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya gabanin zaben.

An gudanar da sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiyar a Otal din Kempinski domin tabbatar da zaman lafiya a yayin zaben 2024.

A ranar 7 ga watan Disamba za a guduanar da zaben na shugaban kasa a kasar ta Ghana.

Kafin sanya hannu, Mahama ya tabbatar da cewa jam’iyyarsa ta himmatu wajen tabbatar da zaman lafiya, yana mai kiran zaman lafiya a matsayin ginshikin da ake gina dimokuradiyya akai.

Bawumia a nasa bangaren ya jaddada mahimmancin tabbatar da cewa an gudanar da zabe ba tare da tashin hankali ba.

Ya bayyana fatan cewa dukkan 'yan Ghana za su bi tafarkin da yarjejeniyar zaman lafiyar ta shimfida.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG