Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kebe Kwanaki 16 Don Fadakarwa Kan Cin Zarafin Al'umma


Tattaki kan cin zarafin al'umma
Tattaki kan cin zarafin al'umma

Majalisar wakilai ta yi wani tattaki na musamman domin wayar da kan jama’a akan cin zarafin dan adam musamman ma mata.

Kakakin Majalisar Wakilai Tajuddeen Abass ne ya jagoranci tattakin wanda ya kai su ga Ofishin Sufeto Janar na rundunar 'yan sandan Najeriya, Kayode Egbetokunm inda suka nemi goyon bayan kawar da duk wani nau’i na cin zarafin mata.

Tattakin ya hada sama da mutane 1,000 yawancin su mata da suka hada da 'yan majalisar wakilai da sauran jama’a.

Daya daga cikin Mmta da suka hallarci tattakin ta mika takardar koke ga Sufeto Janar na 'yan sanda, da neman daukar matakin da ya dace don kare al'umma masu rauni da kuma tabbatar da alhaki ga masu aikata laifukan cin zarafi.

Tattaki kan cin zarafin al'umma
Tattaki kan cin zarafin al'umma

A jawabinsa a lokacin da Sufeto janar na Yansandan Kasa Kayode Egbetokun ya karbe su, kakakin majalisar Tajudeen Abbas ya ce sun zo ne da bukata na ganin 'yan sanda sun yi aikin su, sannan majalisa za ta yi sauran ayyukan da suka shafi 'yan majalisar tare da yin kira da a dauki matakin yaki da cin zarafin mata kai tsaye.

Tajudden ya kara da cewa su a Majlisa sun tsaya tsayin daka wajen yaki da kare hakki da mutuncin dukkan ‘yan Najeriya, musamman wadanda marasa galihu

Tajuddeen ya ce Majalisa za ta hada gwiwa da 'yan sanda wajen yin aiki tare da gyare-gyaren doka da su za su yi, wanda zai taimaka wajen gina al'umma.

A nashi bayanin Sufeto Janar Kayode Egbetokun ya yaba da rawar da Majalisa ta taka wajen ganin an shawo kan cin zarafin al'umma musamman mata.

Egbetokun ya ce ya amince da hada gwiwa da Majalisa wajen aiwatar da dokar ta hanyar hukunta masu laifi.

An kebe kwanaki 16 domin fadakarwa kan matsalolin cin zarafin al'umma musamman mata.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG