Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Zabi Zainab Bagudu A Matsayin Shugabar Kungiyar Yaki Da Cutar Sankara Ta Duniya


Dr. Zainab Bagudu Shinkafi, shugabar gidauniyar Medicaid mai wayar da kai da tallafawa yan Najeriya kan cutar Sankara.
Dr. Zainab Bagudu Shinkafi, shugabar gidauniyar Medicaid mai wayar da kai da tallafawa yan Najeriya kan cutar Sankara.

A jiya Talata, kungiyar yaki da cutar sankara ta duniya ta sanar da zaben Dr. Zainab Shinkafi-Bagudu a matsayin zababbiyar shugabanta a wa’adin shekaru 2 daga 2024 zuwa 2026.

Haka kuma kungiyar ta sanar da zaben sabuwar majalisar daraktocinta mai mambobi 14, sakamakon babban taronta daya gudana ta na’ura a ranar 8 ga watan Oktoban da muke ciki.

Sanarwar da kungiyar ta fitar tace ilahirin mambobinta dake fadin duniya suka taka rawa a zaben, inda ta sake jaddada aniyarta ta hade kan masu ruwa da tsaki a yaki da cutar sankara a fadin duniya.

Dr. Zainab wacce ta fito daga Najeriya ta kasance ‘yar Afrika ta farko da aka zaba a wannan mukami. ita ce ta assasa gidauniyar yaki da cutar sankara ta “Medicaid Cancer Foundation kuma kwararriyar likitar yara ce sannan mamba ce a kungiyar yaki da cutar sankara ta Najeriya wato Nigerian Cancer Society da takwararta ta Amurka American Society for Clinical Oncology.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG