A yau Laraba, Shugaban Najeriya Bola Tinubu, ya bukaci Majalisar Dattawa tayi gyara akan dokar kasafin kudin bana da ta harkokin kudade ta bara ta hanyar kara Naira tiriliyan 6 da biliyan 200 a cikin kasafin kudin bana.
A cikin wasikar, shugaban ya bayyana cewar matakin ya dace da sashe na 58, karamin sashe na 2 na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 da aka yiwa kwaskwarima.
“Anan ina gabatar wa majalisar dattawa da wannan kudiri domin tayi nazari tare da zartar da shi.
“Kudirin dokar kashe kudade ta bana ya nemi a yi gyara akan ainihin dokar da nufin samarda naira tiriliyan 3 da bilyan 200 domin aiwatar da ayyukan raya kasa karkashin shirin “sabunta fata” (renewed hope) tare da sauran muhimman ayyukan raya kasar dake gudana a fadin kasar nan.”
“Sannan naira tiriliyan 3 domin samarda karin kudaden da aka na kashe yau da kullum, wadanda wajibi ne domin gudanar da harkokin kashe kudaden gwamnatin tarayya yadda ya dace, kuma ake sa ran samun daga asusun kudin shiga na gwamnatin tarayyar.”
Tinubu ya kara da cewa ana bukatar yin kwaskwarima akan dokar harkokin kudi ta 2023 ne domin cazar haraji daga irin ribar da bankunan suka samu a hada-hadar musayar kudade kamar yadda bayanan hada-hadar kudadensu ta bara suka nuna.
Tinubu ya ci gaba da cewar an yi haka ne domin samun kudaden gudanar da ayyukan raya kasa da bunkasa ilomi da kiwon lafiya da tsare-tsaren sanya walwala a zukatan al’umma.
Dandalin Mu Tattauna