Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dokokin Kano Ta Zartar Da Kudirin Kirkiro Masarautu 3 Masu Daraja Ta 2


Zauren Majalisar Dokokin Kano
Zauren Majalisar Dokokin Kano

Majalisar Dokokin Kano ta zartar da kudirin kafa masarautu a jihar na bana, domin kirkiro karin masarautu 3 masu daraja ta 2.

Manufar kudirin, wanda Mataimakin Shugaban Majalisar Muhammad Bello Butu-butu ya gabatar shine mayar da masarautar Kano a matsayin mai daraja ta 1, a yayin da masarautun Rano da Gaya da Karaye zasu kasance masu daraja ta 2.

Kudirin ya tsallake karatu na 3 ne a yau Talata yayin zaman majalisar da shugabanta Isma’il Falgore ya jagoranta.

A cewar kudirin, sabuwar Masarautar Rano zata kunshi kananan hukumomin Rano da Bunkure da Kibiya, a yayin da Masarautar Gaya zata kunshi kananan hukumomin Gaya da Albasu da Ajingi, sai kuma Masarautar karaye da zata kunshi kananan hukumomin Karaye da Rogo.

Dukkanin masarautun masu daraja ta 2 guda 3 zasu kasance ne karkashin Sarkin Kano. Suna da ikon baiwa sarki shawara a al’amuran da suka shafi zaman lafiyar jama’a da rikicin kan iyaka da sasanta tsakanin al’umma da al’amuran addinin dake karkashin huruminsu.

Karara kudirin ya tsame Masarautar Bichi, wacce tsohon gwamnan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya kirkira amma dokar masarautun kano da aka yiwa kwaskwarima a bana ta rushe ta.

Kudirin zai zama doka da zarar Gwamna Abba Kabir Yusuf ya rattaba hannu akansa.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG