Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Kasar Rwanda Paul Kagame Ya Sake Lashe Zabe


Shugaban kasar Rwanda Paul Kagame yana kada kuri'a
Shugaban kasar Rwanda Paul Kagame yana kada kuri'a

Shugaban kasar Rwanda Paul Kagame ya lashe zaben shugaban kasar da kashi 99% na kuri'un da aka kada, a cewar sakamakon zaben farko - kashi 79% na kuri'un da aka kada - wanda hukumar zaben kasar ta fitar da yammacin jiya Litinin.

Kagame, wanda ke kan karagar mulki a matsayi daban-daban tun a shekarar 1994, ya samu nasara da irin wannan adadi a shekarar 2017.

Jama’a sun yi hakurin tsayawa kan layi cikin tun daga karfe 7 na safe agogon kasar a ranar Litinin don kada kuri’unsu, suna masu cewa, sun ji dadin gudanar da ayyukansu na ‘yan kasa. Wasu sun shaidawa Muryar Amurka cewa, suna son shugaba wanda zai iya aiwatar da abin da jama'a ke so. Wasu kuma sun ce sun ga ci gaba kuma za su kada kuri'a don ci gaba da hakan.

Wata jami'ar Hukumar Zaben kasar Rwanda tana tantance sunayen masu kada kuri'a
Wata jami'ar Hukumar Zaben kasar Rwanda tana tantance sunayen masu kada kuri'a

Kagame ya kada kuri'arsa da misalin karfe 1:30 na rana agogon kasar gida a wata cibiyar zabe a Kigali. Ya ce abubuwan da ya sa a gaba na gina kasar da kuma bunkasa kasar zuwa wadata ba za su canja ba.

Kagame, wanda aka zabe shi a matsayin shugaban kasa karon farko a shekara ta 2000, ya fuskanci wasu 'yan takara biyu, ciki har da dan takarar jam'iyyar Democratic Green, Frank Habineza da dan takara mai zaman kansa Philippe Mpayimana.

'Yan takarar shugaan kasar Rwanda Frank Habineza, Paul Kagame, Philippe Mpayimana
'Yan takarar shugaan kasar Rwanda Frank Habineza, Paul Kagame, Philippe Mpayimana

Habineza ya zo na biyu da kashi 0.53% na kuri’un da aka kada yayin da Mpayimana ya samu kashi 0.32%.

Wannan shi ne karo na biyu da Mpayimana, dan jarida da ya koma siyasa, wanda aka wallafa manufofinsa na bunkasa noma, sufuri, kamun kifi, da sauran masana'antu a jaridu sama da 50 ya tsaya takarar Shugaban kasa.

Habineza, wanda shi ma ya fafata da Kagame a zaben da ya gabata, ya shaidawa Muryar Amurka cewa, ya sake shiga takarar a bana, saboda Shugaba mai ci ya dade a kan karagar mulki, kuma lokaci ya yi da za a sake alkiblar kasar.

An hana wasu 'yan takara da dama, ciki har da wasu daga cikin masu sukar Kagame, tsayawa takarar shugaban kasa.

Kimanin mutane miliyan 9 ne daga cikin al'ummar Rwanda miliyan 14 aka yi wa rijista don kada kuri'a - wato karin mutane miliyan 2 daga zaben da ya gabata, a cewar hukumar zaben kasar.

Shugabar hukumar zaben Oda Gasinzigwa ta bayyana cewa, sama da masu sa ido na kasa da kasa 300 ne suke kasar Rwanda tare da masu sa ido na cikin gida kusan 700.

Daya daga cikin dalilan da Kagame mai shekaru 66 ya kai ga nasara a cewar masu suka, shi ne ya yi mulkin kama karya da kuma murkushe 'yan adawa. Sai dai wani dalili kuma, in ji manazarta, shi ne kokarinsa na jagorantar kasar da ke gabashin Afirka wajen samun zaman lafiya a cikin gida tun bayan kisan kiyashin da aka yi a shekara ta 1994, lokacin da 'yan Hutu masu tsattsauran ra'ayi suka kashe kimanin 'yan kabilar Tutsi da masu matsakaicin ra'ayi 800,000.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG