Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gobe Jumma'a Za a Gudanar Da Zaben Shugaban Kasa A Rwanda


'Yan takarar shugaban kasar Rwanda
'Yan takarar shugaban kasar Rwanda

Gobe jumm’a kasar Rwanda zata gudanar da zabe, inda ake kyautata zaton shugaba Paul Kagame zai lashe zabe wa’adin mulki na uku. Jam’iyu goma sha daya suka nuna goyon bayan shugaban kasar mai ci yanzu, sai dai har yanzu akwai ‘yan takara da dama dake fafatawa da shi.

Sama da mutane dubu dari biyu suka halarci gangamin yakin neman zabe na karshe da shugaba Paul Kagame ya gudanar. Masu kula da lamura a kasar sunyi kiyasin cewa, zai lashe zaben da gagarumin rinjaye. Ya sami kashi casa’in da uku cikin dari a zaben da aka gudanar cikin shekara ta dubu biyu da goma.

Dan takarar jam’iyar Green Dr.Frank Habineza ya gudanar da gangami farkon makon nan da bai sami halartar mutane sosai ba inda kimanin mutane dari biyar suka halarta. Ana zargin cewa, umarnin da gwamnati ta bayar da ya tilasta a sake wurin gangamin shine ya janyo rashin fitar magoya baya.

Habineza wanda ya kafa jam’iyar ta Green a matsayin wadda zata maye gurbin shugaba Kagame, yana dari darin kushewa shugaba Kagame kai tsaye.

Yace muna sa ido kan tsare tsaren gwamnati. Idan lamura basu tafiya daidai, sai mu kushe a kai, kana kuma mu samar da wata hanyar da za a shawo kan matsalar. Amma ba daidaikun jama’a ba, domin mutum shine yau, ba shine gobe ba, amma gwamnati da al’ummarta suna nan daram.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG