Mai gabatar da kara, wanda aikinsa ne neman sauran masu laifin da ke boye wa kotun duniya da ke shari’ar manyan laifukan da aka tabka a Rwanda, yau Talata ya tabbatar da mutuwar Aloys Ndimbati, wanda ake zargi da aikata kisan kiyashi.
Cikin shekaru uku da su ka gabata, kotun ta kasa da kasa mai shari’ar manyan laifuka ta IRMCT, ta kama wasu ‘yan Rwanda biyu da ake zargi da taka rawa a kisan kiyashi, sannan ta kuma tabbatar da mutuwar wasu masu guje ma kotun su hudu, ciki har da Ndimbati.
A wani bayani, masu gabatar da kara na MDD, sun gamsu cewa Ndimbati ya mutu a Rwanda tun a 1997.
Dandalin Mu Tattauna