Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Daruruwan Mahajjata Suka Mutu Sakamakon Tsananin Zafi A Aikin Hajjin Bana


Mecca, Yuni 16, 2024.
Mecca, Yuni 16, 2024.

Daruruwan mahajjata ne suka mutu bana a yayin gudanar da aikin hajjin shekara-shekara da Musulmi ke gudanarwa a Makka sanadiyar tsananin zafi, kamar yadda rahotannin manema labarai da ma'aikatun harkokin waje suka bayyana.

Akalla mutane 550 ne suka mutu a aikin hajji bana, kamar yadda jami’an diflomasiyya suka shaida wa kafar yada labarai ta Faransa (AFP) ranar Talata. Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, mutane dari uku da ashirin da uku daga cikin wadanda suka mutu 'yan kasar Masar ne, wadanda akasarinsu sun mutu ne sakamakon rashin lafiya da ke da alaka da zafi, a cewar wasu Larabawa biyu jami'an diflomasiyya.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya kasa tantance wadannan kididdigar nan take. Turereniya, gobarar tantuna da dai sauran hadurra sun yi sanadin mutuwar daruruwan mutane a aikin hajjin a Saudiyya cikin shekaru 30 da suka gabata. An fara gudanar da aikin Hajji ne a ranar Juma'a.

Tashar talabijin ta kasar Saudiyya ta bayyana cewa a ranar Litinin din nan ne ma'aunin yanayin zafi ya haura zuwa 51.8 a cikin masallacin Harami da ke Makkah.

Wani bincike na 2024 da Jaridar Travel and Medicine ta gudanar ya gano cewa hauhawar yanayin zafi a duniya na iya wuce duk dabarun magance zafi. Wani bincike da aka yi a shekarar 2019 da Geophysical Research Letters ya yi ya nuna cewa yayin da yanayin zafi ke tashi a kasar Saudiyya sakamakon sauyin yanayi, mahajjatan da ke aikin hajji za su fuskanci “mummunan hadari”.

‘Yan kasar Tunisia 35 ne suka mutu a lokacin wannan aikin hajjin, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Tunisiya Afrique Presse ya sanar a ranar Talata.

Yawancin wadanda suka mutun sakamakon tsananin zafi ne, kamar yadda ‘yan uwansu suka bayyana a shafukan sada zumunta, yayin da sauran iyalai ke ci gaba da neman wasu ‘yan uwansu da suka bace a asibitocin Saudiyya.

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Jordan ta ce ta bayar da izinin binne mahajjatan kasar Jordan guda 41 a ranar Talata. Tun da farko, ma'aikatar ta ce akalla 'yan kasar Jordan shida ne suka mutu sakamakon tsananin zafi lokacin aikin hajji.

Iraniyawa 11 ne suka mutu yayin da 24 ke kwance a asibiti yayin gudanar da aikin hajjin, kamar yadda kafar yada labarai ta Iran IRINN ta sanar a ranar Talata ba tare da bayyana musabbabin mutuwar ba.

Haka kuma wasu ‘yan kasar Senegal uku sun mutu yayin aikin hajji, in ji Agence de Presse Sénégalaise a ranar Litinin.

‘Yan kasar Indonesiya dai dari da arba’in da hudu ne suka mutu a yayin aikin hajjin, kamar yadda bayanai daga ma’aikatar lafiya ta Indonesia suka nuna a ranar Talata. Bayanan dai ba su fayyace ko wasu daga cikin mace macen sakamakon tsananin zafi ne ba.

-Reuters

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG