Wannan Matsala dai tasa ana ganin dogayen layin Alhazan a wasu wurare da hukumar Alhazan Najeriya ta sanya likitoci domin duba lafiyar Alhazan.
A bana dai hukumar Alhazan Najeriya ta hana jami’an Alhazai na jihohi bude sashen kula da lafiyar Alhazansu a masaukansu dake birnin Makkah, da yawa daga cikin Alhazan da Muryar Amurka ta zanta dasu sun koka akan tsawon lokacin da suke dauka kafin ganin likita a Asibitocin, Alhaji Sani Yarima wanda ya raka wata marar lafiya yace sun kwashe sa’o’i sama da Hudu suna bin layi cikin rana mai zafi kafin samun ganin likita.
Darakatan kula da ma’aikatan Harkokin Addinai ta jihar Neja, Umar Faruk Abdullahi, yace tasrin bai yi ba saboda haka ya yi kira ga Hukumar Alhazan Najeriya da tayi gyara akan lamarin. Amma sakataren Hukumar Alhazan Najeriya Dr, Bello Tanbuwal, yace Hukumomin kasar Saudiyya ne suka basu umurnin hana jihohin Najeriya bude guraren kula da lafiyar Alhazansu, saboda haka yace suna kokarin yin gyara akan Matsalolin da aka samu, a halin da ake ciki kuma Amirul Hajji na jihar Neja, janaral Idris Garba mai ritaya ya bayar da sanarwar rasuwar sakataren kwamitin aikin hajjin bana da gwamnatin jihar Neja ta kafa Alhaji Haruna Kusharki a ranar Laraba a birnin Makka sakamakon Rashin Lafiya.
Saurari cikakken rahoton Mustapha Nasiru Batsari daga Makka.