Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dambarwar Masarautar Kano: CISLAC Ta Yi Kira Ga Daukar Matakin Gaggawa Wurin Maido Da Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali


Gwamna Kabir yayin da karbi
Gwamna Kabir yayin da karbi

Cibiyar inganta aikin majalisar da rajin yaki da cin hanci da rasahwa ta CISLAC, ta bayyana matukar damuwa ga dambarwar dake faruwa na sake maida Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu a kan karagar mulki, da kuma sauke Alhaji Aminu Ado Bayero.

CISLAC ta yi kashedi cewa abubuwan dake faruwa na barazanar jefa jihar Kano cikin rikici da tashin hankali, lamarin da zai kawo rashin zaman lafiya a yankin arewacin Najeriya.

Babban Daraktan CISLAC, Auwal Musa Rafsanjani, ya yi gargadi da kakkausar murya kan duk wani yunkuri na amfani da lamarin wajen ayyana dokar ta-baci a jihar Kano. Ya ce, "Ana kallon irin wadannan ayyuka a matsayin rashin tunani da kuma takala wanda zai iya wargaza tarihin siyasar Kano na sama da shekaru 1,000."

CISLAC ta lura cewa hukuncin kotu mai tattare da cece-ke-ce da jami’an tsaro suka dogara da shi ya taimaka wajen dawo da Sarki Aminu Bayero. Alkalin da ya zartar da hukunacin yanzu haka ba shi a cikin kasar kana ba shi kan aikinsa.

“Halin da ake ciki ya haifar da muhimman batutuwa a kan hallaci da cancantar hukuncin kotun, in ji Rafsanjani.” Dogaro da abin da CISLAC ta kwatanta da ‘umarnin kotun cin zali’ wurin tura ‘yan sanda da jami’an tsaro suka mamaye jihar Kano ya yi matukar tada hankali da kuma rura fitina.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, gwamnatin jihar na da hurumin nadawa da kuma tabbatar da sarakunan gargajiya, ciki har da babban Sarkin. “Rafsanjani ya jaddada cewa ba za a lamunta da duk wani yunkuri na kwace wannan hurumi da kuma jefa jihar cikin rikici ba. “CISLAC ta yi imani cewa Gwamnatin Jihar Kano tana da ‘yancin shawo kan matsalolin dake addabar masarautunta kuma dole ne a mutunta wannan ‘yancin domin kaucewa fadawa rikici.”

CISLAC ta yi kira ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da kar ya yarda da duk wani yunkuri na ‘yan siyasa dake neman kawo cikas ga zaman lafiya da hadin kai a jihar Kano. “Bai kamata gwamnatin tarayya ta bari a yi amfani da ita a matsayin makamin da za a cimma muradun siyasa kana a kara dagula zaman lafiyar jihar da yankin, Rafsanjani yana kashedi.”

A matsayinta na mai fafutukar tabbatar da dimokuradiyya da zaman lafiya, CISLAC ta tsaya tsayin daka wajen yin Allah wadai da duk wani nau’i na tashin hankali da cin zarafin hukumomi a jihar Kano. Kungiyar ta yi kira ga dukkan muhimman hukumomin da su ba da fifiko kan tattaunawa da neman hanyoyin da suka dace wajen magance wannan rikici.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG