Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Fasinjoji A Hanyar Nasarawa Zuwa Abuja


Yan bindiga
Yan bindiga

‘Yan bindiga sun yi awon gaba da fasinjojin dake kan hanyarsu zuwa Abuja daga jihar Enugu, bayan da suka kaiwa motar safa da suke tafiya a ciki mai cin fasinja 18 hari a jihar Nassarawa.

Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Nassarawa, Dsp Ramhan Nansel, ne ya bayyanawa tashar talabijin ta Channels hakan.

Nansel, wanda ya bayyana hakan a daren ranar Juma’a, yace ‘yan sanda sun samu bayanin cewar an kaiwa wata motar safa mai cin mutane 18 dake kan hanyarta ta zuwa Abuja daga jihar Enugu hari a kauyen Doruwa, dake kan hanyar Nassarawa zuwa Keffi tare da yin garkuwa da mutanen da ba’a san adadinsu ba.

Ya kara da cewar daga bisani an yi nasarar kubutar da 3 daga cikin mutanen bayan da ‘yan sanda da jami’an sauran hukumomin tsaro suka kaddamar da samame a yankin.

Ya cigaba da cewar, “yan sanda, da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro, sun kaddamar da martanin gaggawa, saidai harin ya riga ya faru gabanin su samu labari. An bi sahun ‘yan ta’addar tare da karade yankin. sakamakon hakan, an yi nasarar kubutar da mutane 3, tare da kwato wasu ababen hawa zuwa caji ofis”.

Nansel ya bada tabbacin cewar hukumomin tsaro ba zasu saurara ba, kuma za’a ci gaba da aikin ceto sauran mutanen da aka yi garkuwa dasu tare da kama batagarin.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG