Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wale Edun Ya Gabatarwa Tinubu Kiyasin Abinda Mafi Karancin Albashi Zai Lakume


Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, a ranar Ma'aikata ta Duniya
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, a ranar Ma'aikata ta Duniya

Ministan Kudin Najeriya, Wale Edun, ya gabatar da kiyasin kudaden da za’a kashe wajen biyan mafi karancin albashi ga Shugaban Kasa Bola Tinubu.

Ministan ya gabatar da kiyasin kudaden ne ga shugaban kasar a fadarsa ta Aso Villa dake Abuja a yau Alhamis, biyo bayan wa’adin sa’o’i 48 da aka bashi akan yin hakan a Talatar data gabata.

Rahotanni na cewar rahoton ya zayyana dimbin zabin matakan biyan mafi karancin albashin tare da tasirin hakan ga kasafin kudin gwamnatin tarayya akan kowanensu.

A ranar Talata data gabata ne Ministan yada labarai na Najeriya, Mohammed Idris ne ya bayyana cewa Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya umurci Ministan Kudi na kasar, Wale Edun, da ya gabatar da tsarin da gwamnati za ta bi na aiwatar da sabon adadin albashin ma’aikata mafi karanci.

Ministan yada labarai, Mohammed Idris (Hoto: Facebook/Ministry of Information)
Ministan yada labarai, Mohammed Idris (Hoto: Facebook/Ministry of Information)

“Shugaban kasa ya umurci Ministan Kudi da ya yi lissafi, ya gano yadda al’amarin zai kasance cikin kwana biyu, ta yadda za mu samu alkaluman da za mu sake tattaunawa da kungiyar kwadago”, acewar ministan.

Ministan ya kara da cewa “Shugaban kasa ya kuduri yin aiki da duk abin da kwamitin ya amince da shi. Ya kuma duba yadda zai kyautata walwalar ‘yan Najeriya.”

Idris ya kuma ce gwamnati ba ta adawa da karin albashi.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG