Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Nijar Ta Maida Wa Jamhuriyar Benin Martani Kan Hana Jigilar Danyen Manta


Fira Ministan gwamnatin Rikon kwaryan Jamhuriyar Nijar, Ali Mahaman Lamine Zeine
Fira Ministan gwamnatin Rikon kwaryan Jamhuriyar Nijar, Ali Mahaman Lamine Zeine

Gwamnatin rikon kwarya ta Jamhuriyar Nijar ta maida martani bayan da shugaban kasar Benin Patrice Talon ya dauki matakin hana lodin danyen man da Nijar ke shirin fara shigarwa kasuwannin duniya a tsakiyar watan Mayu.

Matakin rufe iyakar da Nijar ta dauka duk da dage takunkumin ECOWAS ya sa shugaba Talon tsaurara matakin a matsayin martanin da ke hangen tankwaso mahukuntan Nijar su canza ra’ayi.

A taron manema labaran da ya kira, Firai Minista Ali Lamine Zeine, ya fara da maida martani game da jerin matakan da shugaba Patrice Talon ya dauka akan Nijar wadanda suka hada da hana fitar da kayan abinci daga Jamhuriyar Benin, da matakin hana lodin danyen mai da Nijar ke shirin fara fitarwa ketare daga tashar jirgin ruwan Seme.

A washe garin taron shugabannin kasashen yammacin Afrika da ya gudana a Abuja a watan Fabrairun 2024, wanda ta janye takunkumin da CEDEAO ta kakaba wa Nijar, hukumomin mulkin sojan kasar a nasu gefe sun rufe iyaka da Benin saboda dalilan tsaro, matakin da shugaba Patrice Talon ya nuna rashin gamsuwa da shi, amma Firai Minista Zeine ya jaddada cewa suna da hujjojin da ke gaskanta hasashensu.

A ranar Litinin da ta gabata ne gwamnatin Jamhuriyar Benin ta aike wa jakadan China a Cotonou takarda domin sanar da shi cewa kasar ba za ta bar tankoki su dauki danyen man da Nijar ke shirin fara fitarwa zuwa ketare ba.

kwana daya da ayyana wannan kudiri shugaban kasar ta Benin Patrice Talon a hirarsa da tashar Talabijin ta kasar ya yi karin haske kan wannan lamari, ya na mai cewa ya rubuta wa mahukuntan Nijar takarda don sanar da su cewa Benin ta bude iyaka amma ba a tanka masa ba, haka kuma ya turo da ministan harkokin waje akan bukatar farfado da hulda a tsakanin kasashen biyu nan ma ba su amsa ba, a saboda haka ya zama wajibi Jamhuriyar Benin ta dauki mataki a matsayin martani.

Dambarwar da ta kunno kai a washe garin juyin mulkin da sojoji suka yi a Nijar ta yi matukar tabarbarar da hulda a tsakanin hukumomin Nijar da na makwafciyarta Jamhuriyar Benin.

Saurari cikakken rahoton:

Nijar Ta Maida Wa Jamhuriyar Benin Martani Kan Hana Jigilar Danyen Manta
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:11 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG