Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tasirin Tallafin Naira Dubu 5 Da Gwamnatin Najeriya Ke Bayarwa Bashi Da Yawa - Bankin Duniya


Bankin Duniya ya bayyana tasirin tallafin Naira dubu 5 da gwamnatin tarayyar Najeriya ke rabawa a matsayin marasa yawa ga bukatun iyalai da harkokin banki.

Bankin Duniyar ya bayyana haka a rahotonsa na baya-bayan nan, mai taken, “alheri ya zo” ko “beta don come” a turacin broka: tasirin bada tallafin kudade akan mata da iayalai a Najeriya”.

A cewar rahoton, tallafin nada takaitaccen tasiri akan sana’o’i, musammam ma akan mata.

Rahoton ya bada misalin da shirin bada tallafin kudade na shekarar 2016, sa’ilin da gwamnatin tarayyar Najeriya ta kaddamar da shirin bada tallafinta na NASSP.

A yayin kaddamar da shirin, rahoton yace gwamnatin tarayyar ta samarwa iyalai tallafin Naira dubu 5, inda ake bada su a dunkule duk bayan wata 2.

Rahoton ya kara da cewar, ana biyan kudaden tallafin ne ta hannun wadanda ragamar kulawa da iyalan ke hannunsu, galibinsu mata.

Saidai rahoton ya bada shawarar cewar akwai bukatar samun wata sana’ar da zata rika tallafawa tallafin domin inganta samu da dogaro da kan iyalan.

Bankin Duniyar ya kara da cewar duk da nasarar da ake ikirarin shirin bada tallafin kudaden ya samu, babu wata shaida ko guda dake nuna tasirin kasancewa a cikinsa.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG