Hukumomi da masu sauraron shirye-shiryen gidajen rediyo na yabawa tasirin rediyo ga wayar da kan jama'a cikin sauri da sauki musamman a kasashe masu tasowa da ke da karancin lantarki.
Wannan na zuwa ne a ranar tunawa da Rediyo ta Duniya ta bana.
Taken ranar na bana shi ne " Rediyo kafar sadarwa ta karni wajen sadarwa, nishadantarwa da ilmantarwa " da ke nuna har yanzu ba a samu wata kafa da ta goge tasirin rediyo ga wayar da kan jama'a cikin sauri da sauki ba.
A Najeriya Ministan Labaru, Muhammad Idris, a wata sanarwa da ya fitar, ya bayyana cewa gwamnati za ta bunkasa kafafen labarun cikin al'umma don karfafa dimokradiyyar kasar.
Hukumar raya ilimi da al'adu ta majalisar dinkin duniya UNESCO ta bullo da wannan rana da ta fara daga 1946 inda bayan tuntubar masu ruwa da tsaki a 2011 a ka amince da fara bukin ranar don karrama kafar da a ka shafe shekaru ba tare da kawar da tasirin ta ga miliyoyin mutane a fadin duniya ba.
A shekara ta 2013 a ka aiyana duk ranar 13 ga watan Febrerun kowace shekara ta zama ranar bukin karrama rediyo ta duniya.
Shugaban kungiyar muryar ma'abota kafafen labaru don cigaban kasa Buhari Yunusa Kumurya ya ce tasirin rediyo ya wuce samun labaru don ta hanyar rediyo a kan kulla zumunci a tsakanin masu sauraro na garuruwa daban-daban.
Ita ma mai sharhi Aisha Yasmin ta ce duk da bullowar kafafen labaru na yanar gizo amma ta fi gamsuwa da rediyo don tsarin tace labaru masu sahihanci da rediyo ke da shi.
Zaidu Bala Kofa Sabuwa da ke jagorantar kungiyar Muryar Talaka da ke da membobi da ke hulda da gidajen rediyo ya ce rediyo ne ke zama hanyar samun labaru ga talakawa da kan yi amfani da 'yan batura don samun labaru na tsawon lokaci.
Shugaban Muryar Amurka Aliyu Mustapha Sokoto ya ce kafafen labaru ko ma musamman Muryar Amurka na nan ne don ba da labaru na gaskiya da a kan samu daga majiyoyi masu tushe.
Dandalin Mu Tattauna