Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Kasa Tinubu Ya Karrama ‘Yan Wasan Super Eagles Da Lambar Girmamawa Ta Kasa Ta (MON)


'Yan wasan Super Eagles a fadar Shugaban Kasa
'Yan wasan Super Eagles a fadar Shugaban Kasa

Shugaban Kasa Bola Tinubu ya karrama tawagar Super Eagles da lambar girmamawar ta kasa ta MON saboda bajintar da ta nuna a gasar cin kofin nahiyar afrika ta AFCON da aka kammala a baya-bayan nan a kasar Ivory Coast.

An kuma baiwa kowane daga cikin ‘yan wasan kyautar gida da fili a babban birnin tarayyar Najeriya, Abuja.

Najeriya ta zo a mataki na 2, inda tayi rashin nasara a hannun mai masaukin baki kasar Ivory Coast, wacce a karshe ta lashe gasar.

A talatar nan ne fadar Shugaban Najeriya ta karbi bakuncin tawagar ta Super Eagles inda ta karramasu da lambobin girmamawa.

Eagles In Aso Villa
Eagles In Aso Villa

Dukkanin mambobin da masu horas da kungiyar sun halara a liyafar ciki harda Alex Iwobi, wanda ya fuskanci tsangwama a yanar gizo saboda rashin nasarar tawagar a hannun Ivory Coast.

Shugaba Tinubu Ya Karbi Bakuncin 'Yan Wasan Super Eagles a fadar Shugaban Kasa
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:18 0:00

A saurari rahoton Umar Farouk:

Shugaban Kasa Tinubu Ya Karrama ‘Yan Wasan Super Eagles Da Lambar Girmamawa Ta Kasa Ta (MON)
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:30 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG