Al'umar yankin Tudun Biri da ke karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna sun fuskanci iftila'in harin jirgin sama da aka ce mara matuki ne da ya saki bama-baman da su ka yi sanadin rasa rayuka sama da hamsin sannan wasu da dama suka jikkata a daren ranar Lahadi.
Malam Samuel Aruwan, mai kula da ma'aikatar tsaro ta jihar Kaduna, ya yi karin bayani kan wani taron gaggawa na tsaro da aka kira ranar Litinin, inda ya tabbatar da abin da ya faru.
"Babban kwamandan sojan kasa na Najeriya ya bayyana cewa ba da gangan aka kai harin ba wanda ya kashe bayin Allah da basu ji ba basu gani ba. Lamarin ya faru ne bisa kuskure a yayin da sojojin kasa ke gudanar da ayyuka na musamman don farautar 'yan ta'addan da ke tada zaune tsaye a yankin," a cewar Aruwan.
Daya daga cikin limaman yankin da wani matashi, sun ce da su aka sallaci gawar mutanen da harin bomb din ya hallaka a yayin da suke taron Mauludi. Sun kuma ce an yi jana'izar mutane fiye da 40, ciki har da mata da yara kanana.
Ganin sanarwar rundunar sojan saman Najeriya da ta ce ba ita ta kai wannan hari ba, ya sa shugaban kungiyar Fityanu ta jihar Kaduna Sheik Rabi'u Abdullahi, jan hankali game da abin da ya faru. Yana mai cewa an riga an yi kuskure, yanzu abin da ya kamata shi ne gwamnati ta dauki matakin tallafa wa iyalan da harin ya rutsa da su kuma sojoji su kiyaye aukuwar hakan nan gaba.
Malam Ashiru Ibrahim, shi ma dan garin Tudun Biri ne, ya ce lamarin ya shafi yan'uwansa da dama. A cewar shi, mutane akalla tamanin ne suka mutu sakamakon barin wutar jiragen saman har sau biyu.
Dama dai kananan hukumomin Igabi, Birnin Gwari da Giwa makwabta ne da ke fama da hare-haren 'yan bindiga, lamarin da ya sa jami'an tsaro yawaita yin ayyukan tsaro a yankin don magance matsalar.
Saurari rahoton Isah Lawal Ikara:
Dandalin Mu Tattauna