TASKAR VOA: Alkaluman ofishin kula da basussuka sun nuna cewa yawan bashin da ake bin Najeriya ya tashi zuwa Naira tiriliyan 46.25 a 2022
A cewar wata kungiyar kasa da kasa mai zaman kanta da ake kira ONE, a 2021, yawan bashin da ake bin kasashen Afirka ya kai dalar Amurka biliyan 644.9. Kungiyar ta kara da cewa a karshen wannan shekara ta 2023, kasashen Afirka za su biya dalar Amurka biliyan 68.9 na basussuka, da wasu rahotanni