Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Martani Kan Tabbatar Da Takara Ga Bashir Machina Da Hukumar Zabe Ta Yi


Bashir Machina Da Ahmed Lawan
Bashir Machina Da Ahmed Lawan

Masu sharhi na bayyana ra’ayi kan matakin da hukumar zabe ta dauka na ayyana Bashir Machina a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwani na mazabar Yobe ta arewa a inuwar APC.

Shugaban majalisar dattawan ya tsaya takarar fidda gwani ta shugaban Najeriya amma bai samu nasara ba, inda hakan ya tayar da batun komawa kan kujerar sa ta majalisar dattawa.

Hatta shugaban jam’iyyar Abdullahi Adamu da ke mara baya ga Ahmed Lawan ya gargadi Machina da yin takatsantsan kan kalmomin da ya ke furtawa da su ka saba da muradun jam’iyyar.

Mai sharhi kan lamuran yau da kullum Bashir Baba ya ce wannan wani sauyi ne da ke nuna rashin adalcin makalewa kan mukami ta kowane hali.

Shi kuma masanin kimiyyar siyasa Dr. Farouk BB Farouk ya nuna hakan ba bakon abu ba ne ga jam’iyyu amma ya yi karantsaye ga tanadin dimokradiyya na ba da dama kowa ya tsaya takara matukar ya cancanta.

Za a jira a ga ta inda jagororin APC za su bullowa wannan sabuwar dambarwar da ke kawo musayar kalamai masu zafi.

APC na gwagwarmayar ganin ta dore da mulki bayan saukar shugaba Buhari a 2023 da hakan ke sa daukar matakai masu kawo cecekuce.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:46 0:00
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG