Da yammacin Asabar ido-na-ganin-ido ne 'yan bindiga akan babura su ka afkawa garuruwan Kauran Fawa, Marke da Riheya dake yankin Idasu a Karamar hukumar Giwa, inda su ka dunga harbin kan mai uwar da wabi sannan su ka kone dukiyoyi.
A cikin hirar shi da Muryar Amurka, Malam Ibrahim Shehu Lawal Giwa daya daga cikin al'umar da aka yi jana'izar wadan da su rasu ya ce har yanzu ana neman wasu gawawwaki. Bisa ga cewarshi, 'yan bindigan sun shiga garuruwan ne a kan babura sama da 100, dauke da manyan makamai suka yi ta bude wuta lamarin da ya hana jami'an tsaro shiga nan da nan. Malla Ibrahim Shehu Lawal ya bayyana cewa, banda wadanda aka yi jana'iza, har yanzu ba a ga wadansu mutane ba, wadanda ake kyautata zaton ko dai 'yan bindigar sun yi garkuwa da su, ko kuma sun kashe su.
Ya kuma shaidawa Muryar Amurka cewa, kashe garin wannan harin 'yan bindigar sun sake shiga wani garin suka kashe basaraken.
ran-dan-adam-ba-a-bakin-komai-yake-ba-a-najeriya-atiku
an-soma-fafatawa-don-dakile-ayukkan-yan-bindiga-a-wasu-yankunan-arewacin-najeriya
wasu-yan-bindiga-sun-kai-hari-a-wani-masallaci-a-arewacin-najeriya-suka-kashe-mutane-16
Tuni kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jahar Kaduna Malam Samuel Aruwan ya fidar da jadawali dauke da sunayen wadan da 'yan-bindigan su ka kashe kamar yadda Ya tabbatar.