Babban kotun jihar Bauci ta yankewa wasu mutane biyu Mohammed Sani Alias Bambi mai shekaru 30, da Sabo Rabo wanda aka fi sani da Bullet mai shekaru 40, hukuncin daurin rai da rai a bisa laifin da aka kamasu dashi na yiwa wata mata ‘yar shekary 40 fyade tare da kwakule mata idanu.mai shari;a Rabi Umar a hukuncin nata tace masu laifin wadanda ‘yan saslin Karamar hukumar Toro da Dass ne sun hada baki sukayi wa matar fyade a unguwar Yelwan Dawani dake karamar hukumar Roro a ranar 1, ga wata Maris din shekarar 2012. Inda tace an gurfanar dasu a gabanta ne a ranar 4, ga watan Maris na shekarar 2015 da laifin kulle kulle, fyade da illata mutane da kokarin kisan kai.
A cewarta, wadanda aka yankewa hukuncin da sauran mukarrabansu wanda suka tsere sun kuma cirewa matar, wacce ta kasance gurguwa idonta na dama tare da yiwa idon hagun rauni.
Mai shari’ar tace daya daga cikin wadanda ake tuhumar watau Bitrus Yakubu wanda aka fi sani da Japan ya hadu da ajalinsa a lokacin da yake hannun hukuma a asibitin koyarwa na Tafawa Balewa, inda kuma Usman Sambo wanda akewa lakabi da Galambi dan shekaru 35, shima ana zargin shi amman aka sakeshi saboda rashin shaidu.
Mai shari’ar ta kara da cewa “Masu gabatar da kara sun tabbatar da tuhumar tasu ba tare da wata tababa ba don haka kotun batada wani zabi illa ta yanke musu hukuncin rai da rai ba tare da zabin biyan tara ba. Naji rokon da akeyi na yin afuwa amman ina son sanar muku da cewa wadanda ake tuhuma basu chanchanci a tausaya musu ba domin laifin da suka aikata ya nuna tsantsar rashin Imani da rashin tausayin da sukeda shi, don haka ina yi musu ikirari da shedanu a gangar jikin mutane kuma dole a dauke su daga cikin jama’a.
Wadanda aka yankewa hukuncin da basu amsa laifin su ba sunyi rokon ayi musu sassauci bayan da sukaji hukuncin da mai shari’ar ta yanke sedai kash, bata amsa wanan roko ba illa jaddada hukunci a garesu.
Facebook Forum