An haifi Jariri na farko ta hanyar dashen mahaifa a jihar Texas, dake kasar Amurka, lamarin da aka kwashe lokaci mai tsawo ana gwadawa a kasar Amurka koda shike an taba samun nasarar yin haka a kasar Sweden.
Wata mata da aka haife ta bata da mahaifa ce aka dasawa mahaifar kuma ta hafi jaririn a asibitin koyarwa na jami’ar Baylor, a Dallas. Hukumomin asibitin sun tabbatar da haihuwar jaririn, amma basu bayyana sunan matar kokuma cikakken bayani a kaanta ba.
Asibitin jami’ar ya kwashe shekaru da dama yana gudanar da bincike akan mata marasa mahaifa sama da guda goma wajan dasa masu mahaifa, a shekarar 2016, asibitin ya bayyana cewa an dasa wa mata hudu mahaifa amma an cirewa uku daga cikin hudun juna biyun da suke dauke da shi a sakamakon gudanar jini ta hanyar da bata dace ba.
Asibitin zai bata cikakken bayani akan yawan matan da ya gwada dasa ma mahaifa, mujallar Time Magazine ta bayyana cewa kawo yanzu akwai dashen mahaifa guda Takwas kacal da aka sami nasarar yi, sai kuma wata guda da take dauke da juna biyu a yanzu haka.
Facebook Forum