Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Anga Jiya Anga Yau: Da Shekaru 91 Ta Lashe Gasar Sarauniyar Kyau


Tsohuwa Sarauniyar Kyau
Tsohuwa Sarauniyar Kyau

Krystyna Farley, mai shekaru casa’in da daya 91, da haihuwa ta kammala zangonta na shekara daya a matsayin sarauniyar kyau, mai wakiltar jihar Connecticut a kasar Amurka. A shekarar data gabata ne aka zabeta, a mastayin sarauniyar kyau ta jihar.

A cewar sarauniyar kyau Krystyna, fatar jikinta tana da kyau, hasalima bata shafa komi bayaga janbaki, kuma ita mace ce mai matukar kyau. Da yawa mutane kanyi tunanin cewar, da zarar mutun yakai shekaru 60, musamman mata shike nan tasu ta kare.

Ai kuwa abun ba haka yake ba, a irin tata fahimtar, a dai-dai wannan lokacin nema duniya zata fara. Ta bayyanar da abun da yasa take sha’awar shirin sarauniyar kyau, damace da mutun zai iya nunama duniya cewar yana da kyau, batare da duba ga shekarun mutun ba.

Haka mutun zai iya rawa, da duk wani abu da matashi mai kananan shekaru zai iyayi, an haifeta a gabashin kasar Poland, a shekarar 1925. Tace a wannan lokacin duniya tana kwance basu da wata damuwa.

Bayan zuwan yakin duniya na biyu shine suka fara ganin tashin hankali, kuma bata samu damar nunama duniya irin kyaun da Allah yayi mata ba. Don haka wannan wata dama ce da zata tuna baya, ta kuma ji dadin rayuwar ta, biyo bayan batasamu damar hakan ba a lokacin kuruciyar ta, sanadiyyar yaki.

Ta kara da cewar, babu wata matashiya mace da zatayi tunanin cewar, wai akwai wata mace da ta fita kyau, ko kuma ace mace ba zata gyara jikinta ba, don burge masoya ba, sai dai mace wadda bata san kanta ba. Idan har ace da tsawon shekaru na zan shiga cikin wannan gasar, to babu shakka ‘yan matan wannan zamanin suna iyayin fiye dani.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG