Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matasan 'Yan-Mata Sun Ba Samari Kashi A Gasar Kera Robot


Gasar matasa ta kera mutun-mutumi ta duniya a kasar Amurka, na kara jan hankali, musamman yadda ‘yan mata ke taka muhimmiyar rawa. A ‘yan kwanakin bayane gwamnatin kasar Amurka, ta hana wasu ‘yan mata masu hazaka daga kasar Afghanistan takardun shiga kasar ‘Visa’ har sau biyu.

Abun sai da ya kai shugaban kasar Donald Trump, yasa baki kamin aka basu, babban abun ban sha’awa shine, yadda ‘yan matan ke ba maza kaye a gasar kera ‘Robot’ kimanin kashi 60% na ‘yan mata mahalarta gasar ke jagoranci a baki daya sakamakon gasar

A zantawa da manema labarai, matashiya Samira Bader, ‘yar kasar Jordan, mai shekaru 16, ta bayyanar da cewar, mafi aksarin mutane nada tunanin cewar kera robot aikin matasa maza ne banasu ba, amma a wannan gasar sunaso su bayyanama duniya cewar abun ba haka yake ba.

Haka suma jerin taron ‘yan mata da suke wakiltar kasar Amurka, sun taka muhimiyar rawa, wajen ganin ba’a barsu a baya ba. Matasa daga kasashe 150 a ko’ina a fadin duniya suka halarci gasar.

Matasan dai sun kirkiri robot wanda yake iya banbance fari da baki, kuma yake daukar abu daga wani wuri zuwa wani. An dai yi baji kolin hazaka da babu wani matashi da bazai so ace, yana cikin gasarba, domin kuwa abun ya kawatar matuka.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG