Kamfanin Samsung Electronics ya bayarda sanarwa a yau lahadi cewa zai fara sayarda wani sabon nau’i na wayarsa samfurin Galaxy Note 7 cikin wannan makon a Koriya ta Kudu.
A shekarar da ta shige ne dai kamfanin na Samsung ya janye Galaxy Note 7 daga kasuwa a saboda baturin ciki yana yin zafi ya kama da wuta ko yayi bindiga. Sabuwar wayar zata yi amfani da batura dabam da nau’in masu kama wutar.
Sabuwar wayar, wadda aka sanya mata suna Galaxy Note FE, za a kera ta da kayayyakin da aka kera Note 7, kuma za a sayarda ita a kasuwa a kan dala 611. Wannan kuwa, ba karamin ragi ba ne daga dala dubu daya da aka sayar da Note 7.
Kamfanin Samsung ya janye Note 7 kasa da wata daya bayan fitowarta a kasuwa a saboda rahotannin yadda take kamawa da wuta.
Kamfanin ya sake fitar da wata sabuwar Note 7 da wani sabon baturi, amma su ma sai suka ci gaba da yin zafi da kamawa da wuta. A dalilin haka ne kamfanin Samsung ya janye Note 7 baki daya daga kasuwa.
Facebook Forum