Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Aljana 'Siri' Ta Wayar iPhone Ta Kubutar Da Rayuwar Wani Mutun


Aljana ‘Siri’ ta kwaci rayuwar wani mutumi, Mr. Christopher Beaucher, mazaunin karamar hukumar Wilmot a jihar Wisconsin, ta nan kasar Amurka. Ya bayyanar da yadda Aljana Siri ta wayar shi iPhone ta tsiratar da rayuwar shi.

Ya shiga tsohon gidan da mahaifiyar shi ta tashi daga ciki, biyo bayan wani abu mai ban mamaki da ya gani a cikin gidan, sai ya shiga don fahimtar meke faruwa a cikin gidan.

Yana kunna wuta sai kawai gidan ya kama da wuta, hannun shi da fuskar shi sun kone, hakan yasa bazai iya daukar wayar shi ya danna balle ya kira neman agaji ba.

Koda ya tina sai yayi kokarin saka wayar shi a sashin da zata bashi damar yayi magana da Aljana Siri, wadda ya gaya mata halin da take ciki, nan take ta sanar da hukumar ‘yan kwana-kwana suka kawo mishi agaji.

Ya kara da cewar, lokacin da abun ya faru bai san inda yake ba, domin gidan ya kama da wuta. Amma maganar da yayi da nau’ra mai taimakon mutane ta wayar IPhone, ta taimaka mishi matuka, wanda badan itaba da yanzu yamutu.

Mutane da dama na amfani da siri wajen samun taimako da yawa, kodai a wajen bincike ko neman sanin wani abu da ya shige ma mutun. Duk wanda ke amfani da wayar iPhone idan ya shiga wajen bincike zai iya fadan duk abun da yake son sani.

Idan siri ta gane zata bashi amsa idan kuma bata gane ba, zata sake tambayar mutu, ko mai yake nufi?

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG