Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

A Karshen Wannan Makon Aka Samu Kutse Mafi Girma A Duniya


A hutun karshen makon nan ne dai aka fuskanci babbar matsalar kutse, a fadin duniya. Wannan wani babban kutse ne da ba’a taba samun kamar shi ba. Milliyoyin ma’aikata na kamfanoni, asibitoci, ofisoshin gwamnatoci, da wasu ‘yan kasuwa, sun shafe awowi suna aiki ba kakkautawa, don ganin sun shawo kan matsalar ‘yan kutse.

A karon farko da aka samu wannan matsalar, ma’aikatan kamfanonin sun fuskanci wata barazana, daga ‘yan kutse da suka kirkiri wata manhaja mai suna ‘WannaCry’ suna aika ta zuwa shafufukan kamfanoni don satar bayanai. Duk kuma wanda wannan cutar ta shiga cikin na’urorin su, za’a tambaye su, su biya wani kudi ko kuwa sai sun bada wasu bayanan su kamin cutar ta fita.

Abun dai ya dauki tsawon lokaci ana ta fama da yadda za’a magance matsalar. Manya manya kamfanoni a duniya sun fuskanci wannan matsalar, a shafufukan su na yanar gizo. Hakan ya kara jawo hankalin mutane a fadin duniya, da su maida hankali wajen amfani da shafufukan su na yanar gizo, da duba ga duk irin bayanai da suke aikawa.

Babban mataki da ya kamata mutane su dauka shine, su dinga canza lambobin shiga shafufukan su ‘password’ akai akai. Kana mutane su san irin mutanen da suke mu’amala da su a duniya, da irin maganganun da su keyi a duk lokaci.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG