Ina sana’ar dinkin ne domin na zamo mai dogaro da kai, a cewar wata matashiya ta fara dinkin kayayyakin kawa na mata, don ta tallafawa kanta wajen kashema kanta kananan bukatu, a cewar Ruqqaya Abba Kabara.
Ta ce ta koyi dinkin tumtum, filallika da sauransu, ta ce bayan ta kammala makaranta sakandare ne ta lura zaman kawai ba zai kai ta ga cimma bukatunta da yau da kullun ba.
Ruqayya ta ce ta shafe shekaru hudu tana koyan sana’ar, kuma tana da burin inganta sana’arta, ta hanya kallon talabijin na kasashen wajen, inda suke kawata sana’arsu, da samun wasu basira akan wanda ta koya a wajen koyo, tare da bude shago babban. Kana tana ziyartar shafufukan yanar gizo, don kokarin inganta sana'ar.
Ta kara da cewa kafin ta samu aikin gwamnati, takan samu akalla dinkin yara hamsi a wata, amma a yanzu da ta fara aiki a wata takan samu akalla guda 20, kuma tana yin wannan sana’a ne tare da kanwar mahaifiyarta.
Ta ce hanya daya da mace zata huce wa kanta takaici dai bai wuce dogaro da kai ba.