Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutanen Da Suka Fi Kowa Karfin Fada A Ji A Duniya Na Shekarar 2016


Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin

Da akwai kimanin sama da mutane billiyan 7.4, a doron kasa, a kiyasin jaridar ‘Forbes’ an zakulo maza da mata ashirin 20, da sukafi karfi a duniya. A cikin duk mutane milliyan dari, a duk duniya akwai mutun daya da yafi karfi.

Domin tantancewa, an duba mutane da dama daga kowane irin bangare, na yau da kullun a rayuwa, don zakulo wadanda sukafi shahara a duk fadin duniya.

Anyi amfani da wadansu alkalunma hudu, don tantance su, na daya shine mun tambayi ra’ayin jama’a, ko wadannan mutane suna da mabiyan su, sai adadin karfin kudi da suke mu’amala da, sai duba da yadda suke gudanar da mu’amalar su da al’ummar su ko dai wajen mulki ko taimako.

Na karshe kuwa shine mu tabbatar da yadda mutanen kanyi, amfani da karfin mulkin su yadda ya kamata a tsakanin su da jama’arsu. A wannan shekarar saboda yadda duniya ta shiga cikin wani rudani, masu zaben sun duba matuka don fitowa da wannan sakamakon.

Mutun na farko da yafi karfi a duniya shine, 1) Vladimir Putin, shugaban kasar Rasha, Sai 2) Donald Trump, na kasar Amurka. 3) Angela Merkel, ta Germany, 4) Xi Jinping shugaban kasar China, 5) Pope Francis, shugaban addini Katolik, 6) Janer Yellen, ministan kudin Amurka, 7) Bill Gates, mai kamfanin Microsoft 8) Larry Page shugaban kamfanin Alphabet, 9) Narendra Modi shugaban kasar India 10) Mark Zucherberg shugaban kamfanin Facebook 11) Mario Draghi shgaban bankunan kasashen turai.

12) Li Keqiang Firaministan China 13) Theresa May Firaministan Ingila 14) Jeff Bezos shugaban kamfanin Amazon 15) Warren Buffett hamshakin mai kudin Amurka 16) Salman Bin Abdulaziz Al-Saud, sarkin Saudiya 17) Carlos Slim Helu shugaban kamfanin ‘Group Carso’ 18) Ali Hoseini-Khamenei na kasar Iran 19) Jamie Dimon shugaban bankin JPMorgan 20) Benjamin Netanyahu na kasar Israel.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG