Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amfani Da Yanar Gizo Zai Taimaka Wajen Magance Matsalar Tabin Hankali


Yadda matsalar tabin hankali ke kara zama ruwan dare a duniya, abune da ya kamata a fito da wasu sababbin hanyoyi, don magance aukuwar hakan. Masana na ganin cewar, akwai bukatar amfani da kafafen yanar gizo wajen rage ko magance karuwar matsalar hauka a tsakanin manya da yara.

Kadan daga cikin hanyoyi da suka kamata abi, sune ta yin amfani da shafufukan yanar gizo, ana iya magance cutar, a duk lokacin da aka samar da wani asibiti, da likita zai iya ganawa da mara lafiya ta hanyar sadarwar bidiyo, ko ta magana a rubuce batare da haduwa tsakanin mara lafiyan da likitan ba, hakan zai taimaka matuka wajen rage karuwar matsalar ta tabin hankali.

Idan akayi la’akari da yadda ake kashe makudan kudade, wajen magunguna da dawainiyar masu fama da matsalar hauka, za’a ga cewar abun na kara hauhawa, amma idan ana amfani da yanar gizo, wajen duba mara lafiya da basu duk wasu taimako da suka kamata, zasu iya taimakawa matuka wajen rage yaduwar cutar.

Taron masana cututukan tabin hankali, na yankin kasashen turai, sun kaddamar da wasu kasidu dake nuni da muhimancin amfani da yanar gizo, wajen magance cutar tabin hankali, ganin yadda mutane ke amfani da hanyoyin, don samun sauki akan wasu abubuwa da kan dame su a rayuwa.

Da yawan mutane na yin amfani da kafofin zumunta, kamar su facebook, twitter, instagram, wajen magance damuwar dake tare da su, musamman idan suka samu labari da yake faranta musu rai, dama wasu abubuwa da suka shafi rayuwar su. Don haka masana na ganin cewar, ana iya amfani da wannan damar don rage yawaitar marasa hankali a duniya.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG