Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amina Wali: Muhimmancin Mata 'Yan Jarida A Cikin Al'umma.


Amina Wali
Amina Wali

Shirin Ilimi Mabudin Rayuwa, na DandalinVOA a wannan makon ya karbi bakoncin matashiya Amina Hajia Wali, wadda take karatun digirin ta na farko a jami’ar 'DeMontfort University Leicester' dake kasar Ingila. Amina, na zufafa karatun ta a fannin aikin jarida, sadarwa tare da yaren Faransanci.

Ta bayyanar da dalilin da yasa ta wannan karatun, madadin ta yi karatu a wasu bangarorin da mafi akasarin matasa a wannan zamanin suka fi sha’awar ace suna yi. Kamar su aikin likitanci, kimiyar hade-haden magunguna da makamantansu.

A fahimtarta, mafi akasarin matasa ba sa daukar aikin jarida a matsayin kafa da zasu taimakama al’umarsu, fiye da yadda ake tunani. Domin ta ilmantar da jama’a wasu abubuwa da basu da masaniya ne, kawai zasu iya zama masu iya dogaro da kai da kuma fadada fahimtarsu ta duniya.

Da yawa ma’aikatan jarida sukan fadakar da al’uma, da babu yadda wani zai iya rayuwa ba tare da sanin aikin jarida ba, hakan ya kara bata sha’awa da aikin. A matsayinta na matashiya, da ta tashi a Arewacin Najeriya, tana ganin akwai bukatar ‘yan mata su tashi haikan wajen neman ilimi, musamman na zamani don samun damar iya taimakon kai da kai.

Tace an wuce lokacin da za’a ce mace tana jiran sai iyayenta, ko mijinta yayi mata abu kamin ta yiwa kanta ko ‘ya’yanta. Ta ilmatar da kai ne kawai mata zasu iya ciyar da duniya gaba.

Aikin jarida aiki ne da ya kamata ace mata da yawa a Najeriya su shiga, ganin yadda sauran kasashen da suka ci gaba a duniya ke da matan da suke gogayya da maza a wajen aikin jarida, dama duk wani fannin na ci gaba a rayuwa.

A karshe Amina Wali, na kira ga mata ’yan uwanta, da su tashi tsaye wajen neman ilim, a kowane hali suka samu kansu, don ta haka ne kawai za su iya bada tasu gudunmawa wajen cigaban kasa.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG