Kamfanonin Facebook da na Mozilla, sun shiga cikin jerin sahun kamfanoni, da wasu kungiyoyi da suka kaddamar da wani asusun, dallar Amurka milliyan goma sha hudu $14M, domin kyautata yadda jama’a ke samu da fahimtar labarai, kana da kara amincewa da aikin jarida.
Kungiyar mai zaman kanta, da ake kira ‘News Integrity Initiative’ a turance, masu matsugunni a jami’ar babban birnin New York. Kungiyace mai cin gashin kanta, zata dinga gudanar da ayyukan ta a karkashin tsangayar koyon aikin jarida na jami’ar.
Wasu daga cikin masu bada gudun mawa sun hada da kamfanin Craigslist da gidauniyar Ford. A ‘yan kwanakin nan alkalunma sun bayyanar da yadda mutane, basu da sauran yadda ga kidajen labaru.
Labaran karya da waddanda basu da sahihanci, sukan zama hanyoyi da ke bata inganci labarai. Mafi akasarin labaran karya ana yadasu ne ta kafafen yanar gizo, ganin yadda zaben da ya gabata a kasar Amurka na 2016, ya samu sa’ido a ko’ina a fadin duniya, da wasu labarai mara tushe. Yanzu haka dai kamfanin facebook na kokarin magance irin wannan dabi'ar.