Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Twitter Sun Dakile Wasu Shafufuka Masu Alaka Da 'Yan-Ta'addah.


Kamfanin shafin zumunta na Twitter, sun kulle wasu shafufukan zumunta na mutane sama da 376,000 a farkon shekarar da ta gabata. Mafi akasarin shafufukan ana amfani da su wajen wallafa mugayen akidojin ‘yan ta’adda.

Kimanin kashi saba’in da hudu 74% na shafufukan an dakilesu ne, biyo bayan amfani da wata manhaja, mai suna ‘Proprietary Software’ a cewar kamfanin wannan itace babbar hanyar magance duk wani ta’addanci a duniya, da ‘yan ta’adda kanyi amfani da yanar gizo a fadin duniya, ko hanyar dakile muggan akidoji.

Ita dai sabuwar manhajar da suke amfani da ita, tana lura da yadda mutun ke amfani da shafin nashi, wajen magana da suwa mutun yake bibiya, ko yadda ake taba labaran da masu alaka da ‘yan ta’adda ke sakawa a shafufukan su.

Kashi biyu 2% kuwa na shafufukan, sun samu bayanai ne daga wasu bangarorin gwamnati, dake nuni da alakar su da ‘yan ta’adda. Kimanin yawan shafufukan da suka dakatar a shekarar 2016, sunfi yawan adadin shafufuka baki daya na yanar gizo da aka kulle a shekarar 2015.

Jimilla kamfanin twitter sun bayyanar da cewar, sun kulle shafufuka da suka kai 636,280 daga 1 ga watan Ogusta 2015 zuwa Disamba 31 2016. Wannan ya zone a dai-dai lokacin da kamfanin Facebook da Goggle ke neman hanyar magance irin wannan matsalar a shafufufkan su.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG