Kamfanin zumunta na Facebook na yunkurin bama ma’abota hurda dasu, damar bayyanar da wuraren da suke a yayin amfani da bidiyon kaitsaye. Kamfanin ya sanar da hakan ne da cewar, idan Allah ya kai rai ranar Litinin zasu kaddamar da wannan damar.
Hakan wata damace da zasu bama abokan hurdar su, amfani da ita don bayyanar da cikakkun bayanai akan abubuwa da suke aikatawa, duk da ganin cewar kamfanin Apple sun yi wani abu makamancin hakan.
A iya bincike da suka gudanar sun iya ganin cewar, mafi akasarin ‘yan uwa sukan tambayi ‘yan uwan su, ko suna ina ne a yayin da suke daukar bidiyon kai tsaye, hakan zai basu damar bayyana ma mutane kai tsaye batare da sun tambye suba.
A cewar shugaban sashen cigaban kamfanin Mr. Stan Chudnovsky, wannan wata damace, da mutane kan iya amfani da ita idan bukatar hakan ta taso, amma idan mutun bashi da bukata, zai ya kashe damar. Tun dai a shekarar 2014, kamfanin yaraba bangaren sakon gaggawa na facebook din da ainihin shafin.
Hakan wata damace da suke amfani da ita wajen inganta shafufukan a kowane lokaci aka samu cigaba a duniyar kimiyya.