Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jirgin Ruwa Mai-Amfani Da Hasken Rana Na Farko A Duniya, Zai Fara Shawagi!


Jirgin Ruwa Mai Amfani Da Hasken Rana.
Jirgin Ruwa Mai Amfani Da Hasken Rana.

A Jirgin ruwa na farko mai amfani da hasken rana, a fadin duniya zai tafi shawagi na tsawon shekaru shida. A zagayen da jirgin zaiyi zai zagaye duniya, daga farkon wannan shekarar. Asalin jirgin na tsere ne, wanda aka canza shi zuwa girgi mai amfani da hasken rana.

Jirgin yana dogara ne da wutar da zai samar ma kanshi, daga hasken rana da kuma karfin farfelan dake samar masa da wadatacciyar iska, da zai iya yunkura shi. An kiyasta kudin jirgin da ya kai kimanin dallar Amurka $5.25M dai-dai da naira billiyan biyu da milliyan dari biyar da saba’in.

Jirgin yana bakin gabar teku a yankin Saint-Malo, zai fara tafiya daga gabar Brittany, inda zai yi tsaye-tsaye a kimanin tashoshi dari da daya, wanda suka hada da kasashe hamsin a fadin duniya, zai farawa daga kasar Paris.

cewar Mr. Nicolas Hulot, kwararre a harkar muhalli, yace wannan wani yunkuri ne da yake nuna alamu, akwai nasara wajen kauracema amfani da mai a na’u’rorin tafiye-tafiyen zamani. Ya kara da cewar, duk wata matsala da ta shafi yanayi, duk hanyoyin shawo kan matsalolin suna nan kusa damu, haka dai na nuni da cewar, akwai bukatar zurfafa bincike.

Asalin jirgin an kirkire shi ne a shekarar 1983, karkashin shugabancin Mr. mike Birch, jirgin dai ya samu lashe babbar kyautar Jules Verne a shekarar 1994.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG