WASHINGTON, DC —
Cinikin wayoyin kamfanin Samsung yayi faduwar da ba a taba gani ba cikin shekaru biyar da suka gabata, yayin da kasuwannin hazukan waya ke kara faduwa a kasuwannin duniya.
A jere shekaru uku kenan cinikin wayar Samsung ke ja baya. Samsung ya shiga wani hali bayan da ya tsinci kansa wajen yin kiranyen miliyoyin wayoyin Galaxy Note 7 saboda samun matsalar batiri.
Wannan matsala da Samsung ya samu ta yi sanadiyar asarar Biliyoyin daloli, har ma takai ga kamfanin ya dakatar da kera wayoyin Galaxy Note 7.
Yanzu haka dai Samsung na neman hanyar dawo da cinikin wayoyinsa a kasuwar duniya, inda yake shirin fitar da sabuwar wayar Galaxy S8.