Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabon Mashin "Mutunmutumi" Mai Gani Harhanjin Duniyar Wata!


Sabon Mashin Din Curiosity Rover
Sabon Mashin Din Curiosity Rover

A karon farko hukumar binciken sararrin samaniya NASA, ta fitar da bidiyon yanayin duniyar watan “Mars” wanda mutunmutumin “Curiosity Rover” ya dauka tun bayan tura shi duniyar da akayi shekaru biyar da suka wuce.

Bidiyon dai ya nuna zagayen duniyar na murabba’in 360, wanda aka dauka a ranar biyar ga watan Augusta. Babban abun sha’awa da hoton bidiyon shine, yadda ya bayyanar da tsarin cikin duniyar, ba waje ne da yake a bude ba, yana da tudu da kwari kamar yadda wannan duniyar take.

Mutunmutumin yayi yayo matuka a cikin duniyar, duk da wasu 'yan matsaloli da ya fuskanta, na tsallake wasu tudu da gangara. Haka da wasu abubuwa masu kama da duwatsu sun shiga gaban na'u'rar sau da yawa. Suna kokarin ganin yadda za suyi amfani da mutunmutumin, don kara fahimtar hallitun da suke cikin duniyar ta wata.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG