Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mashin Mai Amfani Da Hasken Rana Ya Zagaye Duniya!


Mashin Mai Amfani da Hasken Rana
Mashin Mai Amfani da Hasken Rana

An kwashe shekaru ana kirkirar motoci masu amfani da hasken rana, ko ace wadda ake cajin ta kamar yadda ake cajin wayar hannu. A karon farko Jerin wasu matasa daliban jami’a a kasar Netherland, sun kaddamar da wani mashin mai amfani da hasken rana. Yanzu haka dai mashin din daai da suka kirkira ya zagaye duniya.

Bas Verkaik, yace sun kirkiri wannan mashin din ne, don nuna karfin mashin, da yadda yakan iya aiki cikin kowane irin yanayi. Ya kara da cewar mashin din da suka kirkira yana iya duk wani abu da mota kanyi, zai yi tafiya fiye da ta kilomita dari shida a rana.

Don kara tabbatar da karfin mashin din da yaddda yake aiki, sun tuka mashin din na tsawon kwanaki tamani 80, babu tsayawa, sun zagaye duniya da shi.

Daga nahiyar Turai, zuwa nahiyar Asiya, suka zagayo nahiyar Larabawa, sai yankin Amurka da Canada. Wannan yunkurin nasu abu ne da yayi dai-dai da matasa a kowace nahiya su maida hankali wajen nuna basirar su.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG