Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Za'a Samar Da Aiki Ga Matasa Milliyan 1, Ta Hanyar Yanar Gizo a Kasar!


Wasu Dalibai a Kasar Kenya
Wasu Dalibai a Kasar Kenya

Hukumomi a kasar Kenya, sun fara wani yunkuri na horas da matasa sama da milliyan daya. Horaswar zata bama matasan damar iya sana’a ko aiki ta hanyar yanar gizo. Hasalima, wannan damar zata bama matasan zarafin gabatar da ayukan gwamnati, ko na kamfanoni a gidajen su batare da zuwa wajen aiki ba.

A cewar babban bankin duniya, kasar ta Kenya, itace kasa da tafi yawan matasa marasa aikin yi, a yankin gabashin kasashen Afrika. Kimanin kashi goma sha bakwai, na matasa a kasar basu da aikin yi. Haka makotan kasashen Tanzaniya da Uganda, suma suna fama da rashin aiki yi da yakai kashi biyar zuwa shida.

Zuwa yanzu haka dai akwai kimanin matasa dubu arba’in, dake aiki ta hanyar yanar gizo, ga wasu manyan kamfanoni a kasashen duniya, wanda suka hada da kamfanin Amazon Mturk, da wani kamfanin kasar ta Kenya KuHustle.

A tabakin ministan labarai, sadarwa kimiyya da fasahar kasar Mr. Joe Mucheru, wannan tsarin bama matasa horaswar sanin makamar aikin yanar gizo, zai taimaka matuka wajen kara yawan matasa masu aikin yi, da zai kai sama da matasa milliyan daya. Wannan wani tsari ne na gwamnatin kasar mai suna Ajira.

Domin kuwa sunyi hasashen cewar, nan da ‘yan shekaru kadan masu zuwa, za’a dena daukar mutane aiki, saboda aiki ta yanar gizo tafi sauki da arha wajen biyan albashi.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG