Kamar yadda muka saba a kowane karshen mako, shirin samartaka na dandalinvoa na kawo maku hira da matasa samari da ‘yan mata akan lamurra daban daban da suka shafi zamantakewa, soyayya, da sauran batutuwa makamantan haka, a wannan satin mun sami zantawa ne da matasan domin jin ra’ayoyinsu akan zaman aure ko soyayya da mara ilimin boko da na addini amma kuma ga tarin dukiya.
Ta dalilin haka ne muka fara da samari kuma sun bayyana ra’ayoyinsu mabanbanta inda kusan kashi saba’in da biyar cikin dari na matasan da muka sami zantawa da su akasai maza uka nuna amincewar zama da mace komi rashin iliminta.
Kamar yadda wasu daga ciki suka bayyana, nauyin ilimantar da ‘ya mace ya rataya akan mijinta koda kuwa iyayenta sun bata ilimi musamman na addini, to amma sai dai lamarin idan da muka koma bangaren mata ya bambanta domin kuwa su ‘yan matan sun bayya cewa babu abin da yafi hatsari kamar ‘ya mace ta sadaukar da kanta wajen auren mara ilimi.
Bugu da kari, auren matashi mara ilimi a cewar wasu daga cikin ‘yan matan da muka sami zantawa da su tamkar sayar da kaine koda kuwa shine mai arzikin duk duniya. Koda shike ba a cewa ga wanda yafi zama mafi sarkakiya ko daure kai, amma dukiya aba ce da kowane dan adan yake alfahari da ita, amma kuma masu iya magana sun ce, ilimi gishirin zaman duniya, kuma garkuwar dana dam.
Ku ziyarci shafinmu na facebook domin bayyana ra’ayi.
Saurari cikakkiyar hirar a nan.