Mata masu harkar kasuwanci a Najeriya, sun koka akan rashin iya ci gaba da gudanar da aiyukansu na kasuwanci, saboda matsalar dallar da ake fama da ita.
Wata karamar ‘yar kasuwa a Najeriya, mai suna Aisha Salisu, tace a yanzu haka wannan hali da ake ciki na matsalar tashin gwauron zabi da dalar tayi ya dukufar da sana’ar da take yi na fita Najeriya, ta saye kayayyakin da take sayardawa.
Ta ce fiye da shekaru bakwai kennan da ta fara sana’a tun canji dala na Naira dari da ‘yan kai, amma kimanin shekara guda da ya wuce sana’ar ta tsaya cak, domin kuwa tun ana hawa jirgi dubu dari da yan kai domin saro kaya a kasashen waje yanzu an ninnika wanda dole ya tilasta aka tsayar da sana’ar.
Aisha ta ce lailai matsalar dala ya karya wa jama’a sana’oi da dama, a cewarta ko da mutum yana da halin saro kayan ba’a samun riba , sannan matsalar bashi ma na jawo koma bayan ga sana’a.
Ta kara da cewa ta karanci ilimin shari’ah bayan auren ta bai samun nasara yadda ya kamata ba, hakan ne ya sa ta dukufa wajen neman nata na kanta, domin kula da kanta da ‘ya ‘yanta dama wasu na kusa da ita.