A yayin da ake gab shiga sabuwar shekara ta dubu biyu da goma sha bakwai, wasu matasa masu sha'awar cigaban kwallon kafa a jihar Bauchi na tarayyan Najeriya sun kirkiro wata kungiya mai suna Bauchi progressive football Association, Karkashin jagoranci Alh Balarabe Douglas.
Ita dai wannan kungiya an kafatane domin taimakawa matasa masu buga kwallon kafa a jihar don ganin an taimaka musu sunci gaba.
Kamar yadda jagororin suka bayana dalilansu na kafa kungiyar sunce an jima ana yunkarin ganin cewa kannensu sunci gaba ta wajan wakiltar jiharsu a wasu manya manyan kungiyoyin kwallon kafa a kasar da ma Sauran kasashe,
ta dalilin haka zasuyi amfani da wannan kungiya wajen sa gasa a tsakanin Kungiyoyin da suke cikinta domin a cire haziqan 'yan wasa da kuma sada zumunci a tsakanin matasan.
A yanzu haka kungiyar tana da kulob kulob sama da Ashirin a karkashinta bayan haka kuma kofarta a bude take ga duk wata Kungiyar da take da sha'awar shiga.
A Bayan zaman da akayi a mitin na uku an fidda suna wadanda zasu jagoranci kungiyar a matsayin rikon kwarya na dan wani lokaci kafin a zabi cikakkun shugabannin da zasu jagoranci kungiyar wanda a ka basu rikon, sune Kamar haka;
Shugaban ta Alh Balarabe Douglas, sai sakataren kungiyar Alh Usman Baba, mataimakin sakatare Abubakar Aliyu Zadawa, Ma'ajin kungiya Mal Munkaila, sauran sun hada da sakataren tsare tsare wanda aka ba Mal Garba Idris, akwai Bala Dahiru, a matsayin Jami'in watsa labarai.
Bayan haka Akwai kwamitin dattawa a kungiyar Wanda yake karkashi jagoranci Mal Asko, tare da Mambobinsa Mal Ado Amah, Tafidan Galadiman Bauchi, da Alh zubairu Gwabba, da Bala Gambo Dass, da kuma Alh Babayo Ofi.