A shirin mu na nishadi a yau mun sami bakuncin Bashir Idris wanda aka fi sani da Mix-Bash, more sauti, mawakin hip-hop na Hausa wato rap, wanda yace yana hip hop, da ragge wato zaurance tun yana makarantar firamare a kungiyoyi irin na makarantu inda ya shiga kungiyar mawaka.
Mix-Bash dai ya bayyana cewa ta dalilin haka ne suka ga cewar ya kamata su sauya salon canza cultural group zuwa na zamani, wato na kirkirar waka tare da yin zaurance a wakokinsu.
Da haka ne sannu a hankali har ya shiga makarantar sakandire inda suke kwaikwayon wakokin fitattun mawaka hip-hop, daga bisani suka kudiri niyyar rubuta wakarsu da kansu domin su rera kamar yadda suke ganin gwarzonsu nayi a wannan lokaci .
Da tallafin malamar su ‘yar kasar Ingila wacce ta mara musu baya suka sami kwarin gwiwa, daga karshe ya ce a yanzu yana wakar hip-hop da zaurance da wasu sababbin salo.