Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Manyan Labarai Da Su Kafi Nishadantarwa A Shekarar 2016!


Karshen Shekarar 2016
Karshen Shekarar 2016

Kowace shekara takanzo da irin nata yanayin, wasu manazarta rayuwa a karni na ashirin da daya 21, sun bayyanar da wasu kadan daga cikin labarai da su kafi samun kauna a yanar gizo, a daukacin shekarar 2016. Labarai ne da suka samu ziyarar mutane fiye da kima.

Labari na farko shine labarin wani matashi dan asalin kasar Japan, Pikotaro wanda yayi fice a harkar barkwanci, ya saka wani bidiyo a shafin youtube, na wakar da yayi ma suna “PPAP, The Wacky Rap Song” wakar itace wakar da akafi kallo a wannan shekarar 2016.

Na biyu kuwa shine labarin shahararren dan tseren kasar Jamaika, wanda ya lashe tseren mitoci 200, a gasar wasannin na Rio Olympics, da aka gabatar a kasar Brazil, wani hoto da ya nemi huda yanar gizo, da ya nuna shi a gaban abokan hamayyar shi. Wanda hakan yake nuna cewar ya shahara a fagen tsere.

A gaba kuwa sai labarin dan tseran cikin ruwa Michael Phelps, wanda aka dauki wani hoton shi cikin fushi, da bacin rai a tsakanin shi da abokin hammayar shi, yayin wasan Rio Olympics.

Labarin wani mai shayi dan kasar Pakistan Chai Wala, ya dauki mutane da ban mamaki, inda aka saka wani bidiyon shi yana fifita shayi na ban mamaki, hakan dai ya jawo mishi sanayya da hakan yasa aka bashi aiki na kwarai.

A gaba kuwa wani bidiyon waka ce da mawakan suke motsi kamar mutane da basu da jini, sai labarin mawakiyar kasar Amurka, Beyonce, wakar ta mai take “Lemonade” wakar dai ta samu karbuwa a ko ina a fadin duniya. Hakan yasa mawakiyar yawon rangadi a yankin arewacin kasar Amurka, don nuna kauna ga masoyan ta.

Yanar gizo wata damace da mutane, musamman matasa zasu iya daukar wata baiwa da Allah, yayi musu, don sakawa wasu su gani, don kara ba wasu karfin gwiwar suma zasu iya kaiwa ga kowane mataki a rayuwa.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG