Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Matasa Sun Kona Ofishin 'Yan Sanda


Wasu gungun matasa sun bankawa wani ofishin ‘yan Sanda wuta a jihar Anambra, dake Najeriya., shi dai wannan ofishin na ‘yan an kusan kammala ginin sa ne a garin Mkpuunando, dake karamar hukumar Anambra ta gabas kafin matasan su banka masa wuta.

Sarkin garin Igwe Alex Edozieuno, wanda ya bayyanawa manema labarai yace tuni ya rubutawa Gwamnan jihar, willie Obiano, da sufeto janar na ‘yan Sandan Najeriya, Ibrahim Idris, akan batun.

Kakakin ‘yan Sandan jihar Mrs. Nkeiru Nwode, wace ta tabbatar da afkuwar lamarin tace rundunar ‘yan Sandan jihar ta baza komarta na neman wadanna matasa da suka aikata wannan aika aika.

Ta kara da cewa babu wanda zai aikata irin wannan laifi a saka masa ido, rundunar zata tabbatar da ganin cewa an damkesu an kuma gurfanar dasu a gaban kuliya.

XS
SM
MD
LG